When preparing your advertisement, you should first define your product's Unique Selling Proposition (USP). |
A lokacin da kake shirya tallar ka, yakamata ka fara ayyana Shawarar Siyarwa ta Musamman (USP). |
To find the USP, ask yourself "How is this product different?" |
Domin samar da USP, ka tambayi kanka "Ta yaya wannan samfurin ya kasance na daban?" |
Make a list of your product's pros and cons. |
Ka shirya jerin fa'idodi da fursunonin samfurin ka. |
This will help you think about what message you want your ad to send. |
Hakan zai taimaka maka wajen tunani akan wani sako kake so tallace ka (ad) zai isar. |
Positioning is an attempt to place a product into a certain category in consumers' minds: "the best", for example (best deodorant, best soda, etc.) ("The best" is, however, extremely difficult to establish for a new brand). |
Daidaita matsayi wani yunkuri ne na sanya samfur a cikin wani nau'i a tunanin masu amfani: "mafi kyawu", misali (mafi kyawun deodorant, mafi kyawun soda, da sauransu) ("Mafi kyawu" shine, duk da cewa, yana da matukar wahala a kafa sabon alama). |
Types of positioning are Against (eg, Hertz vs. Avis, 7-up vs. colas), Niche (a sub-division of a category), New, and Traditional. |
Nau'in daidaita matsayi sun ci karo (misali, Hertz vs. Avis, 7-up vs. colas), Niche (wani yanki na rukuni), Sabo, da na Gargajiya. |
A Brand Character Statement sets the tone for an entire campaign. |
Bayanin Halayen Samfur yana bayar da sauti ga gabaki ɗaya kamfen ɗin. |
A simple way to start preparing your advertisement is with this statement: "Advertising will ____A_____ ____B_____ that ____C_____ is ____D_____. Support will be ____E_____. Tone will be ____F_____." where A is a verb, B is a target demographic (such as, "girls between 14-18 years old"), C is your product, D is an adjective or phrase. |
Hanya mai sauƙi don fara shirya tallan ka shine yi tare da wannan bayanin: "Talla zai ____A_____ ____B_____ cewa ____C_____ shine ____D_____ Tallafin zai zama ____E_____. Sautin zai zama ____F____." inda A shine fi'ili, B shine alƙaluman manufa (kamar, "'yan mata tsakanin shekaru 14-18"), C shine samfurin ka, D siffa ne ko jumla. |
E is what the meat of your ad will be. |
E shine abin da naman tallan ka zai kasance. |
F is your ad's "attitude". |
F shine "ɗabi'ar" tallace ka. |
For example, "Advertising will convince artistic types age 18-35 that Apple computers are hip and cool. Support will be two men discussing Macs and PCs. Tone will be humorous." |
Misali, "Talla za ta jawo hankalin nau'ikan fasahar masu shekaru 18-35 cewa kwamfutocin Apple zafafa ne kuma masu ƙayatarwa. Gudummawa zai zama maza biyu suna tattaunawa akan Macs da PC. Sautin zai zama abin ban dariya." |
Part B of this strategy statement is the target audience. |
Sashen B na wannan bayanin dabarun shine masu sauraro da aka yi niyya. |
Advertisers use many methods to gain information about this group, including demographics, psychographics (how the target thinks), and focus groups. |
Masu talla suna amfani da hanyoyi da yawa don samun bayanai game da wannan rukunin, waƴanda suka haɗa da ƙididdiga na alƙaluma, ilimin halayyar ɗan adam (yadda waƴanda akayi niyya ke tunani), da ƙungiyoyin mayar da hankali. |
Part C is the product itself. |
Sashe na C shine samfurin da kansa. |
Advertisers spend time studying this as well. |
Masu talla suna ɗaukar lokaci suna nazarin wannan kuma. |
Important questions to ask are "Why would anybody buy this?" "What's the product's advantage?" and "What is the client's image?" |
Tambayoyi masu mahimmanci da za a tambaya sune "Me yasa wani zai sayi wannan?" "Mene ne amfanin samfurin?" kuma "Mene ne alamar abokin ciniki?" |
The last one is important to consider in order to make sure that your ad doesn't jar with the public perception the company has created for itself. |
Na ƙarshe yana da mahimmanci a yi la'akari da shi don tabbatar da cewa tallan ka bai cika ra'ayin jama'a da kamfani ya ƙirƙira don kansa ba. |
For example, hip or edgy ads probably won't go over well with a company that has a public image of being "conservative" and/or "family friendly." |
Alal misali, tallace-tallace masu hip ko edgy ba zasu yi kyau ba ga kamfanin da ke da hangen jama'a na kasancewa "mai ra'ayin mazan jiya" da / ko "mai sauyuwa ga iyali". |