The quiet game is a children's game where children must stay quiet. |
Wasan shiru wani wasan yara ne da ake bukatar yara su yi shiru |
Stillness is sometimes a rule but in most cases not. |
Wani lokacin nutsuwa kan kasance a cikin dokokin wasan, amma wasu lokuta, ba haka ba ne. |
The last child or team to make noise wins the game. |
Wanda ke nasara a wasan shi ne yaro ko tawagar karshe da ta yi kara ko magana. |
It is usually acceptable for players to make sounds they cannot control, such as sneezing whereas talking would cause a player to get out. |
Yawancin lokuta an yarda masu wasa su yi kararrakin da ba za su iya dakilewa ba, kamar su atishawa, amma idan dan wasa ya yi magana, ya fita kenan. |
The game is often played indoors, typically in classrooms. |
Yawanci ana wasan ne a cikin daki, musamman ma kamar Ajujuwa. |
It can also be played outdoors, for instance, at summer camps. |
Amma ana iya yin wasan ma a waje, misali a sansanonin bazara. |
One application of the game is for parents to keep their loud children quiet for a long journey. |
Daya daga cikin muhimmancin wasan shi ne domin iyaye su iya sanya 'ya'yan su masu surutu su kasance sun yi shiru a yayin tafiya mai nisa. |
It is often used as a social discipline. |
Yawanci ana amfani da shi a matsayin hanyar horo a cikin jama'a. |
There is no writing to others in the silent game because it would count as talking to others. |
Ba a yi wa juna rubutu a wannan wasan shiru saboda ana daukan hakan a matsayin magana. |
The objective of the game is to get opponents to giggle or talk by any means necessary. |
Manufar wasan shine a sanya abokan hamayya su yi dariya ko magana ta kowacce hanya |
This can include but is not limited to making funny faces and gentle tickling. |
Wannan ya kunshi amma bai tsaya akan yin fuskokin abun dariya da cakulkuli. |
A person cannot make another make noise by inflicting bodily harm. |
Mutum ba zai iya sanya wani ya yi kara ko magana ba ta hanyar jikkata shi |
There are many versions of this game, but nonetheless follow the same general rules: one who talks is immediately eliminated (laughing included), eventually isolating the winner at the end. |
Akwai salo daban daban da ake yin wannan wasa, amma duk da haka dokar daya ce:duk wanda ya yi magana ya fita (har da dariya), ta haka za a fitar da wanda ya ci nasara a karshe. |
Sometimes it is played with the words in the dictionary instead of all sounds. |
Wani lokacin ana amfani da kalmomin da ke cikin kamus a maimakon kowacce irin kara. |